fidelitybank

Babu wanda ya isa ya sauke ni daga muƙami na – Ayu

Date:

Shugaban babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, Dakta Iyorchia Ayu, ya jaddada matsayinsa na shugaban jam’iyyar tare da cewa, babu wanda ya isa ya sauke shi daga muƙaminsa.

Mista Iyorchia Ayu ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da yake ganawa da al’umar ƙabilar Jemgba a gidansa da ke Karamar Hukumar Gboko a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Shugaban Jam’iyyar dai na takun saka da wasu gwamnonin jam’iyyarsa ciki har da gwamnan jiharsa ta Benue Samuel Ortom, wanda ke ta kiraye-kirayen ya sauka daga muƙaminsa.

Ya ƙara tabbatar wa mutanen cewa babu abin da zai sa ya sauka daga mukaminsa .

“Jam’iyyar PDP guda ɗaya ce. Ina bakin ƙoƙari na wajen ganin ban ɓata wa al’umar Benue da na Najeriya ba. Dan haka idan kun ji suna ta kiraye-kirayen saukeni daga muƙamina, to kar hakan ya dame ku, babu wanda ya isa ya saukeni daga kan kujerar shugabancin jam’iyyarmu. Kawai zan bar kujerar ne ranar da Allah ya kaddara saukata”, in ji Iyorchia Ayu

dailypostnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp