fidelitybank

Babu saɓani tsakanina da mataimakina – Gwamnan Neja

Date:

Gwamnan Neja Mohammed Umaru Bago ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa akwai saɓani mai girma tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba, inda ya ce babu abin da ke tsakaninsu sai dai fahimtar juna da girmama juna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya karɓi karramawar gwarzon ma’aikata a bikin Ranar Ma’aikata da aka yi a Minna.

“Wannan duk raɗe-raɗi ne kawai ake yaɗawa. Muna da fahimtar juna sosai da mataimakina, kuma babu abin da zai iya shiga tsakaninmu. Burinmu shi ne samun nasara, kuma za mu same ta,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Bago ya samu rakiyar Sanata Mohammed Sani Musa ne, wanda yake wakiltar Neja ta Gabas a majalisar dattawa.

Sai dai ya ce wasu ayyukan masu muhimmanci ne suka sa mataimakinsa bai samu damar halartar bikin ba.

the nation newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp