fidelitybank

Babu rikici tsakanin ƙabilu a Kagarko – Gwamnan Kaduna

Date:

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta bayanan da ke cewa an yi sulhu tsakanin al’ummar Hausa da Fulani da kuma Koro a ƙaramar hukumar Kagarko sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakanin su.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta fitar yau Litinin, wadda ta samu sa hannun Muhammad Lawal Shehu, mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.

Sanarwar ta ce tana jan hankalin al’umma daga wasu rahotannin da babu gaskiya a cikin su, waɗanda ke bayyana cewa ministar mata ta Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi wani zaman shiga-tsakani da manyan ƙabilun, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen rikicin da aka kwashe shekara 20 ana fama da shi a yankin.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa “Kagarko na daga cikin ƙananan hukumomi mafiya kwanciyar zaman lafiya da lumana a jihar, kuma an kwashe shekaru ba tare da wani rahoton na rikici a ƙaramar hukumar ba.”

Sanarwar ta ce wasu tsirarun mutane ne suka tunkari ministar da batun, kawai domin cimma wasu muradu na ƙashin kansu.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp