Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel, ya nanata cewa, dan wasan baya Joao Cancelo ya ji dadi a kungiyar a daidai lokacin da ake rade-radin danganta shi da Arsenal.
Cancelo, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Bayern Munich daga Manchester City, ana alakanta shi da komawa Arsenal a kakar wasa ta bana.
Dan wasan, mai shekaru 28, ya kasa samun tagomashi a Manchester City, kuma kociyan kungiyar Pep Guardiola ya yanke shawarar sallamarsa a watan Janairu zuwa Bayern Munich.
Da aka tambaye shi game da makomar Cancelo a taron manema labarai kafin wasan ranar Juma’a, Tuchel ya fadawa manema labarai: “Ina da ra’ayin cewa yana jin dadi sosai a nan. Amma a Æ™arshe, dukkanin bangarorin suna cikin shawarar.
“Burinsa a horon na musamman ne. Ina jin cewa yana farin ciki sosai a nan. Za mu tattauna komai bayan karshen kakar wasa. “