Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, kuma Darakta-Janar na Kungiyar Kamfen din Shugaban Kasa, Rotimi Amaechi, Sanata Ali Ndume, APC, Borno ta Kudu ya yi watsi da maganar Shugaba Buhari, yana mai cewa dimokradiyya ce.
Da yake magana da jaridar Vanguard, Sanata Ndume wanda ya bayyana cewa, babu laifi Buhari yana son ya zabi wanda zai gaje shi, ya ce, babu wani shugaban da ba zai bayyana sunan wanda zai gaje shi ko kuma ya yi sha’awar wanda zai gaje shi bayan mulki.
Ndume wanda ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya zabi mataimakinsa, Joe Biden domin ya gaje shi, kuma yayi aiki tukuru wajen marawa Biden baya, ya ce babu laifi a matsayin shugaba Buhari idan ya yi haka.