fidelitybank

Babu isashun takardar buga sababbin kudi – CBN

Date:

Gwaman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin ba shi da isassun takardun da zai ishe shi buga sababbin kuɗin da ake buƙata a ƙasa.

Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron majalisar magabata ta ƙasar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Jaridar PREMIUM TIMES.

Gwamnan Babban Bankin ya shaida wa majalisar magabatan cewa hukumar da ke lura da buga takardun kuɗin ƙasar ba ta da isassun takardun buga sababbin kuɗin, abin da ya sa aka kasa buga wadatattun takardun kuɗi da aka sabunta a ƙasar.

“Hukumar ba ta da takardun da za ta buga 500 da 1,000. Amma sun yi odar takardar daga ƙasashen Jamus da Birtaniya, to sai dai har yanzu layi bai zo kansu ba kasancewar akwai layi a odar, dan haka odarsu ba za ta samu yanzu ba”, in ji Emefiele.

Ya ƙara da cewa “CBN ya buƙaci hukumar da ke buga kuɗin da ta buga kofin takardu miliyan 70, abin da zai isa a buga naira biliyan 126 da za a sake su, su zagaya hannun mutane a wannan rana ta Juma’a, to amma hukumar ba ta da isassun takardun da za ta yi wannan aiki”. Kamar yadda majiyar ta shaida wa jaridar PREMIUM TIMES.

A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya alƙawarta cewa za a shawo kan matsalar cikin kwana bakwai.

Tuni dai wasu jihohin ƙasar sun shigar da ƙarar gwamnatin tarayya da Babban Bankin domin ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Lamarin da ya sa Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki, lokacin da za ta yanke hukunci kan lamarin.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp