Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Honarabil Hamisu A Faru mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta kudu a majalisar dokokin jihar ya ce “babu yadda za a yi sulhu da mutumin da bai san Allah ba”.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan da ‘yan bindigar suka kori mazauna wani kauye gaba ɗayansu a cikin ɗaya daga ƙananan hukumomin da yake wakilta kana suka mayar da shi sansaninsu.
Dan Majalisar ya ce “Gwamnan jihar ya fito ya ƙalubalanci duk wani mai neman a yi sulhu da ‘yan fashin” wanda hakan ne ya ƙara musu ƙarfin gwiwa a wannan tafiya.
Ya ce akwai firgici a halin da ake ciki a jihar yanzu, domin ɓarayin sun tsallaka titin Gurusu sun bi Barayar zaki sun tsallaka Gulbi sun je wani ƙauyen Rafin Gero da ake ce masa Gyaɗo sun yi sansani, yau tsawon kwana goma kenan.
Ya kara da cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne an shiga damuna, lokacin da yaƙi da waɗannan mutane ke ƙara tsananta.
Da yawan dazuka itatuwansu sun yi kore sun zama duhuwa, tsakaninka da mutane ba tazara mai yawa amma duhu ba zai barku kuga juna ba.
“Shekaran jiya sun shiga kauyukan Ruwan rana da Yashi sun ƙona shaguna da kuma dukiya mai yawa,” in ji Hamisu A Faru.