fidelitybank

Babu batun maganar baiwa ASUU Naira dubu 10 – PTA

Date:

Kungiyar iyayen yara da malamai ta ƙasa, ta karyata maganar cewa za ta bayar da gudunmawar Naira 10,000 kowannensu ga kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, domin kawo karshen yajin aikin na watanni 6.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Haruna Danjuma ya fitar, ya nesanta kungiyar daga wannan ikirarin.

Ya yi bayanin cewa PTA ba ta da masaniyar wannan furucin, ya kuma gargadi wani ko wasu jama’a da su yi amfani da sunan su wajen kawo rudani a kasar nan.

A cewar sa, “Ba mu da hannu a duk wata sanarwa da ta shafi biyan kudi ga ASUU domin su janye yajin aikin da suke yi.”

Ya kara da cewa, “A matsayinmu na tun da aka fara yajin aikin, shi ne kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya su cimma matsaya, wato a kawo karshen yajin aikin amma ba wai a ba da kudi don biyan ASUU ba.

Yayin da yake kira ga gwamnatin tarayya da ta saurari bukatar ASUU, shugaban PTA ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta kubutar da duk daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su da sauran ‘yan Najeriya a fadin kasar nan da ke hannun ‘yan bindiga.

Danjuma ya koka kan halin da ake ciki a Yawuri, inda har yanzu dalibai mata da aka sace suna hannun ‘yan bindiga sama da kwanaki 400.

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp