Jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima ya karyata labarin da ke cewa, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) na shirin hadewa kafin nan da zaben shugaban kasa na 2023.
Galadima wanda ya yi magana a shirin talabijin na Arise a ranar Litinin din da ta gabata ya ce sabanin rade-radin mutane, cewa ‘yan takarar shugaban kasa biyu suna tattaunawa ne kan “ kawancen zabe, ba hadewa ba.
Jigo a jam’iyyar NNPP wanda ya ce shi ne ya jagoranci kwamitin sasantawa ya bayyana cewa dukkanin bangarorin biyu suna da fahimtar kusan dukkanin batutuwan da aka tabo sai daya – wato wanda ya kamata ya zama dan takarar shugaban kasa, da kuma wanda ya kamata ya tsaya masa.
Ya ce, “Ba mu tattauna batun hadewa da jam’iyyar Labour ba. Abin da muke tattaunawa akai shi ne kawancen zabe tsakanin dan takarar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party da dan takarar jam’iyyar Labour.
“Na jagoranci tattaunawar na tsawon sa’o’i 13 masu kyau kuma muna da fahimtar kusan dukkanin batutuwan da aka gabatar sai daya – wanda ya kamata ya zama dan takarar shugaban kasa, da kuma wanda ya kamata ya tsaya masa.”
Galadima ya kuma bayyana cewa wadanda ke cewa “cin mutunci ne” su nemi Peter Obi ya tsige Kwankwaso “ba ‘yan siyasa ba ne,” domin da su ‘yan siyasa ne, da ma ba su yi mafarkin hakan ba.
Ya kara da cewa yayin da kungiyar Peter Obi ta fara watanni biyu kacal da suka wuce, kungiyar Kwankwaso ta “Kwankwasiyya Movement” ta shafe shekaru 32 tana mulki.