fidelitybank

Babu batun ƙara kuɗin makaranta ga ɗalibai – Gwamnatin Tarayya

Date:

Fadar shugaban kasa, ta ce, babu batun ƙarin kudin karatu (tution fee) a ckin kuɗaɗen da jami’o’in gwamnatin tarayya ta ƙarawa ɗalibai.

Dele Alake, mai ba shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

A baya-bayan nan ne mahukuntan Jami’ar Legas suka ƙara kuɗaɗen makaranta da dalibai za su biya daga N19,000 zuwa N190,250 ga daliban da ke karatun likitanci kuma N140,250 ga daliban da ke karatun sauran kwasa.

Wannan ya haifar da wasu martani yayin da mutane da dama suka soki matakin, wanda ya zo a lokacin da ake fama da raɗaɗin cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu yayi.

Sanarwar ta ce “A farkon makon nan ne wasu kafafen yada labarai suka yada labarin cewa Gwamnati ta ƙara kudin karatu a jami’o’in gwamnatin tarayya a kasar nan.”

“Waɗannan rahotannin ba daidai ba ne. Muna sane da cewa wasu jami’o’i a ‘yan makonnin da suka gabata sun sanar da karin kudin da dalibai ke biya na makaranta.”

“Sai dai kuma mun tabbatar da cewa wadannan kudade da jami’o’i suka ƙarawa dalibai na wurin kwanan dalibai ne da sabuwar rijistar da akeyi duk bayan zangon karatu da dakin gwaje-gwaje da sauran kuɗaɗe amma banda kudin karatu (tution fee) a ciki.”

“Mahukuntan wadannan jami’o’in ma sun bayyana wannan hujjar sosai wajen bayyana dalilan da suka sa akayi ƙarin waɗannan kudade don gujewa shakku.”

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya ci gaba da jajircewa kan alkawarin da ya dauka na ganin kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikin iyayensa ba, ya samu damar samun ingantaccen ilimi a manyan makarantu.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp