Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce babu abin da zai hana a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnatin Tinubu addu’a domin samun nasara.
Ya yi wannan jawabi ne a wani taron tattaunawa da sarakunan gargajiya da na addini wanda bankin duniya ya shirya ranar Laraba a Abuja.
Karanta Wannan: Osinbajo ya fi Tinubu cancantar mulkar Najeriya – Peter Obi
Ya ce: “Dole ne a samu canji domin nan da ‘yan kwanaki ko makonni masu zuwa za a samu sabuwar gwamnati; me za mu iya ba wa waccan gwamnatin don ta daidaita?
“Ko kowa ya so, dole ne a yi shi, sabuwar gwamnati za ta zo a ranar 29 ga Mayu, don haka me za mu yi banda addu’a, saboda mun yi imani da Allah Madaukakin Sarki, mun yi imani da Allah mai bayarwa da karba.
“Bayan haka me? Me za mu yi don taimakawa gwamnati ta daidaita da ciyar da kasar gaba?
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai su yi aiki domin tabbatar da gaskiya da adalci.