fidelitybank

Babbar Magana: ‘Yan Bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar yi kasa hidima ta NYSC

Date:

 

Wasu ƴanbindiga ɗauke da muggan makamai sun sace tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya, NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu ya tabbatar wa BBC cewa an sace Manjo Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Laraba da daddare.

”An sace shi ne tare da wasu mazauna garin 13 ciki har da mata biyu, a lokacin da maharan suka auka wa garin, kodayake daga baya mutum huɗu sun kuɓuto”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Duk da cewa ƙaramar hukumar Kankara na fama da matsalolin ‘yanbindiga, amma garin Tsiga bai saba fuskantar irin wannan matsala ba.

To amma kwamishinan tsaron ya ce a baya-bayan nan sau uku masu garkuwa da mutane na shiga garin tare da sace mutane.

Kwamishinan tsaron ya kuma yi zargin cewa masu tsegunta wa ‘yanbindiga bayanai ne suka tsegunta musu shigar tsohon Janar ɗin zuwa garin ”saboda a ranar Laraba da rana ne ya shiga garin, kuma da daddare suka je suka ɗauke shi”.

”Daga bayanan da muka samu tsohon janar ɗin bai je garin da rakiyar jami’an tsaro ba, ya je ne da direbansa kawai”, a cewar kwamishinan.

Ya kuma gwamnati ce da jami’an tsaro na ƙoƙari domin tabbatar da ceto mutanen da ‘yanbindigar suka sace.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp