Babban Limamin Oyo, Sheikh Mashood Abdul Ganiyy Adebayo Ajokidero III ya rasu.
DAILY POST ta tattaro cewa, ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis.
Wata majiya ta kusa da iyalin ta ce, “Assalamu alaikum. Innalillah wainna Ilaihu raajiun. Muna Sanar Da Rasuwar Babban Limamin Oyo. Allah ya saka masa da Jannatul Firdausi. Amin”.
Har yanzu ba a cika samun cikakken bayani game da rasuwar malamin addinin musuluncin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.