Babban layin wutar lantarki na kasa da kamfanin tura wutan lantarki (TCN) ke gudanarwa ya durƙushe a safiyar yau, Alhamis, lamarin da ya jefa kasar baki ɗaya cikin duhu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa faɗowar na zuwa ne makonni kadan bayan da kamfanin tura wutar lantarki (TCN) ya yi bikin shafe sama da shekara guda ba a samu durƙushewar wutar lantarki a Najeriya ba.
Wata sanarwar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu (EEDC) ya fitar, ta ce ɗurƙushewar ta afku ne da misalin karfe 12:40 na safe wanda ya yi sanadin daukewar wuta a faɗin ƙasar.
“Saboda wannan lamarin na durƙushewar layin wutan lantarki a Nageriya, duk tashoshinmu na TCN ba su da wadatar tura wuta wanda hakan yasa ba za mu iya tura wuta ga abokan cinikinmu a jihohin Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo ba.”
Wannan dai shi ne karon farko da aka fuskanci matsalar durƙushwar babbar layin wuta na ƙasa a karkashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.


