Babban layin wutar lantarki na kasa ya samu matsala, inda aka ɗauke wuta a kafatanin ƙasar a jiya Lahadi 12 ga watan Yuni.
Wannan lamari shi ne karo na huɗu da babban layin wutar lantarkin ya samu matsala tun watan Afrilun da ya gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wani kamfanin wutar lantarki ya ce an ɗauke wutar ne da misalin ƙarfe 6 na yamma bayan da wutar da ake samarwa a tasoshi daban-daban a fadin ƙasar ta ragu.
Kamfanin rarraba wutar lantarkin na ƙasa TCN ya ce, wutar da ake samarwa ta ragu amma bai faɗi abin da ya jawo hakan ba.
A ranar 12 ga watan Mayu ma sai da babban layin wutar lantarkin ya samu matsala, inda mafi yawan yankunan ƙasar suka rasa wuta.
Sannan ranar 8 ga watan Afrilu ma matsalar ta sake faruwa ciki har da babban birnin ƙasar Abuja. In ji BBC.