Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, ya yi ikirarin cewa ya yi wa kansa caca ta hanyar karbar aiki a Stamford Bridge.
An nada Pochettino a matsayin kocin na dindindin na Blues a bazarar da ta wuce bayan an kore shi a Paris Saint-Germain.
Dan kasar Argentina, wanda kuma ake alakanta shi da Real Madrid da Manchester United, ya ce ya san aikin Chelsea zai zama “babban kalubale”.
Ya ce: “Na yi wasa da sunana na zo Chelsea kuma, a wani aiki da ya shafi gina kungiya mai matasa, hazikan ‘yan wasa wadanda za su iya zama manyan ‘yan wasa.
“Mun san cewa wannan babban kalubale ne amma ina so in ba kungiyar kayan aikin don cin nasara wasanni, imani da kanmu, da gina kyakkyawar dangantaka”.
Nasarar da Chelsea ta samu a kan United da ci 4-3 a ranar Alhamis, ta haura zuwa mataki na 10 da maki 43.