A ranar Alhamis ne babban alkalin jihar Oyo, Munta Abimbola, ya kafa kwamitin mutum bakwai da zai binciki zarge-zargen da majalisar ta yi wa mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Majalisar dai na yunkurin tsige Olaniyan, matakin da ya kara tsananta, bayan da mataimakin gwamnan ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.
Gwamnan jihar, Seyi Makinde da mafi yawan ‘yan majalisar jihar suna cikin jam’iyyar PDP.
Olaniyan ya yi zargin cewa, Makinde ya yi watsi da shi tare da mayar da shi bayan gwamnatinsa kafin ya sauya sheka.
Sai dai an kafa kwamitin ne, bisa ga kudurin majalisar, kuma kamar yadda kakakinta Adebo Ogundoyin ya bukata.
Ogundoyin ya yi wannan bukata ne a wata wasika mai kwanan wata 6 ga Yuli, 2022.
Shugaban majalisar a cikin wasikar, ya bukaci kundin tsarin mulkin kwamitin bisa ga ikon da aka bai wa babban alkalin jihar ta sashi na 188 (5) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999.
Mambobin kwamitin sun hada da Cif Kayode Christopher (Shugaban); Adebisi Soyombo; Cif Lawal Adekunle Dauda; Gimbiya Olanike Olusegun; Rev Fr. Patrick Ademola; Cif Mrs Wuraola Adepoju (JP); da Alh. Tirimisiyu Akewusola Badmus.