Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya wanke kuma ya sallamin tsohon Sakatare Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal daga zargin satar kuɗin sare ciyawa.
A ranar Juma’a ne Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta wanke Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga zargin badaƙalar kuɗi naira miliyan 544 da aka tanada don gyara sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Mai Sharia’a Charles Agbaza ya ce babu wani abu da ya nuna cewa Babachir yana da laifi a cikin bayanan da shaidu 11 da EFCC ta gabatar suka bayar.
Sai dai, cikin wata sanarwa EFCC ta ce tana shirin karɓar kwafin shari’ar da zimmar ɗaukar mataki na gaba.
“Saboda ba ta ji daɗin hukuncin ba, EFCC ta nuna alamun cewa za ta karɓi kwafin shari’ar don nazarin gaggawa da kuma ƙalubalantar sahihancinsa a Kotun Ɗaukaka Ƙara,” in ji kakakin EFCC Wilson Uwujaren.