Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ba zai yarda shugaban jam’iyyar na ƙasa Iyorcha Ayu ya jagoranci gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 a jiharsa ba.
Wike na wannan maganar ne a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a Fatakwal babban birnin jihar.
“An cuci mutanen Ribas sakamakon zaluncin da aka yi musu,” in ji shi yayin da yake jawabi a ranar Asabar.
Mista Wike ya ƙara da cewa: “Na faɗa na maimaita, Ayu ya yi ƙaurin suna wajen cin hanci da rashawa, don haka ba zan bari mutum mai hali irin wannan ya jagoranci gangamin yaƙin neman zaɓe a jihata ba”.
Gwamna Wike da sauran gwamonin PDP huɗu na son Ayu ya sauka daga muƙaminsa a matsayin hanyar sasanta rikicin da suke yi da ɗan takarar shugabancin ƙasa Atiku Abubakar.