Sanata mai wakiltar yankin Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawa, Obinna Ogba, ya musanta shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), gabanin babban zabe mai zuwa a jihar.
Ku tuna cewa Ogba ya tsaya takarar gwamna a jihar Ebonyi a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, amma daga baya ya sasanta da abokin hamayyarsa, Ifeanyi Chukwuma Odii, wanda yanzu shine dan takarar gwamna a jam’iyyar a jihar.
Sanata Ogba na mayar da martani ne kan rade-radin da ake ta yadawa a jihar cewa yana da shirin ficewa daga PDP zuwa APC bisa zargin an hana shi samun tikitin jam’iyyar a jihar.
A cewarsa: “Ni dan jam’iyyar PDP ne, kuma babu abin da zai sa in fice daga jam’iyyata zuwa APC,” in ji shi