Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ba za ta shiga yajin aiki ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Atiku ya ce, gazawar gwamnati na warware yajin aikin ASUU ba zai taba faruwa a karkashin gwamnatin sa ba.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron tunawa da ranar matasa ta duniya na shekarar 2022 a Abuja ranar Juma’a.
Atiku ya jadadda cewa mafi muhimmanci kuma hakki na kowane matashi shi ne ‘yancin neman ilimi.
Ya ce: “Saboda haka, na yi watsi da yajin aikin ASUU. Rashin iyawar gwamnati na magance wannan rikicin ba zai taba faruwa a karkashin gwamnatin PDP ko gwamnatin da zan sa ido a kai ba.
“Na kasance ina saka hannun jari a fannin ilimi tun shekaru 30 da suka gabata.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin hada hannu da hukumomin jami’ar wajen ganin an kawo karshen yajin aikin da ake fama da shi.
“Na yi imanin PDP ta samar muku da mafi kyawun tsarin da za ku iya aiwatar da burin ku na gama gari,” in ji shi.
ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen mutunta yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009.


