Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ce har yanzu yana kan matsayarsa, cewa ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da ‘yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.
”An yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so”, in ji gwamnan.
”Saboda haka ina nan a kan bakata, maganar sulhu da ‘yanbindiga babu ita”, kamar yadda ya bayyana
Ya ce duk da haka, ƙofa a buɗe take ga ƴan fashin da ke neman hanyar da za su dawo su rungumi zaman lafiya, ta hanyar miƙa wuya kuma su kawo makamansu ga hukuma.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ‘yanbindiga ke yawaita kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane.