Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana rade-radin da ake ta yadawa kan burinsa na neman shugabancin kasar.
El-Rufai ya bayyana cewa duk da cewa ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa, bai taba tattaunawa da kowa irin wannan shiri ba.
Ya yi wannan tsokaci ne a gidan talabijin na Arise TV a yammacin ranar Litinin yayin da yake tsokaci kan tarurrukan da ya yi da ‘yan adawa.
A kwanakin baya ne El-Rufai ya gana da wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar Kaduna. Ya kuma yi ganawa da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da jam’iyyar Social Democratic Party, SDP.
Sai dai tsohon gwamnan ya yi watsi da yiwuwar komawa PDP.
A cewar El-Rufa’i: “Duk wanda ya kai shekara 35 da ya mallaki takardar shaidar kammala sakandare to ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa, don haka ta haka ne na cancanta.
“Amma na fara magana da kowa game da tsayawa takara kowane ofis? A’a ban taba tattaunawa da kowa ba.
“PDP ba jam’iyya ce da zan yi tunanin shiga ba. Na yi tunani tuntuni na yanke shawara. Babu wani abu da ya canza.”