Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya shaidawa al’ummar jihar cewa, ba zai taba kasawa wajen gudanar da ayyukan sa na gwamna ba.
Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da dimbin magoya bayansa a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi domin murnar nasarar da ya samu a kotun daukaka kara da ke Sakkwato a ranar Juma’a.
Gwamnan ya sanar da jama’a cewa a shirye ya ke ya kara baiwa al’ummar zabe ribar dimokuradiyya ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa da za su yi tasiri kai tsaye ga rayuwarsu, musamman na talakawa.
Ya ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya nuna cewa da gaske bangaren shari’a na gudanar da aikinsu na kungiya mai zaman kanta, domin yin adalci ga kowa da kowa ba tare da nuna bambancin kabila, siyasa ko addini ba.
Yayin da yake yabawa kotuna bisa yadda suke gudanar da ayyuka nagari, Idris ya bukaci su ci gaba da tafiya domin tabbatar da dimokuradiyyar kasa da kasa baki daya.
“Wannan hukunci ya nuna cewa an ba su wa’adin mutanen Kebbi. Wannan ya nuna cewa mutanen Kebbi suna da tunani mai kyau ga Kauran Gwandu, shi ya sa Allah Madaukakin Sarki ya na tare da su,” inji shi.