Shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya Iyorchia Ayu ya ce ko a jikinsa game da kiraye-kirayen da wasu suke yi cewa ya sauka daga kan mukaminsa.
Kazalika ya ce, masu yin hakan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba.
A hirarsa da BBC, tsohon dan Majalisar Dattawan ya ce, a iya saninsa ‘yan kasar ne suka zabe shi bisa sharuddan da jam’iyyarsu ta shata.
Ya kara da cewa, ko a lokacin da za su gudanar da zaben shugabannin PDP na kasa, an yanke cewar ba za a yi la’akari da bangaren da shugaban jam’iyyar ya fito ba wurin fid da dan takarar shugaban kasar.
An jima ana kai ruwa rana tsakanin jam’iyyar da dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a zaben fid da gwani, wato gwamnan Rivers Nyesom Wike, wanda rahotanni suka ce ya gindaya sharuddan ci gaba da zama jam’iyyar, da kuma mara wa Atiku Abubakar baya a matsayin dan takararta a zaben 2023.
Daga cikin sharuddan akwai bukatar Shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Arewacin Najeriya ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai a martanin da ya yi da BBC ta tambaye shi, Mr Ayu ya ce ba bu inda za shi, la’akari da cewa an zabe shi ne bisa dokokin da jam’iyyar PDP ta shimfida, a don haka ba zai sauka ba saboda kawai wasu ba sa son ganin shi a kai.


