fidelitybank

Ba zan sake zama shugaban ƙasa ba a Najeriya – Goodluck

Date:

Yayin da ake ta kiranye ya dawo kan mulki, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa ba.

Jonathan ya ce, ba zai iya sake tsayawa takarar Shugaban kasa ba saboda an kore shi a zaben 2015.

Tsohon Shugaban kasar ya ce, zai rage wa kansa ne ta hanyar zabar fom ya fara jan hankalin mutane da sake yakin neman zabe.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani littafi mai suna ‘My Time As Chaplain in Aso Rock’ wanda Nathaniel Bivan ya rubuta, wanda ya yi cikakken bayani kan tarihin Chaplain na Aso Rock Villa Chapel a zamanin Jonathan, Obioma Onwuzurumba.

An gabatar da littafin ga jama’a a ranar Talata.

Sai dai da yake tsokaci a kan kungiyar da ta sayi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a kan Naira miliyan 100, Jonathan ya ce, ya ji dadi domin ba zai sake zama shugaban kasa ba.

Wata kungiya da makiyaya da almajirai sun saya wa Jonathan fom din tsayawa takara a APC Naira miliyan 100 gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Jonathan ya ce, “Na ji dadin sosai. Ko kadan basa zagina. Bayan haka, an kore ni daga ofishin cewa ban isa ba. Don haka, idan yanzu ’yan Najeriya suna cewa, ‘Oh, mutumin nan ya zo,’ wato suna share ni. Don haka.

“Idan kun tashi gobe kuma ku ga cewa ni ne Shugaban kasa kuma, hakan yana nufin akwai yiwuwar an sami wasu yanayi da suka fi karfina. Amma ba wai a je a dauko fom daya a je a fara rarrashin jama’a da yin yakin neman zabe ba, ko mulki na PDP ne ko tsintsiya madaurinki daya da APC ta zarce a fadin Najeriya. Ba zan iya sake yin hakan ba; idan na yi haka, zan rage kaina.”

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...
X whatsapp