Tsohon shugaban ƙasar Amurka kuma ɗan takara a zaɓen nan mai tafe Donald Trump ya ce matuƙar ya faɗi zaɓe a wannan karon, to ba zai sake tsayawa takara ba.
Wannan ne karo na uku da Trump mai shekara 78 yake yi wa jam’iyyar Republican takara a jere.
A wata tattaunawa da ya yi da rukunin kafofin sadarwa na Sinclair, da aka tambaye shi ko yana tunanin sake yin takara idan Kamala Haris ta doke shi, sai ya ce, “Ba na tunanin haka,” in ji shi.
Sai dai ya ƙara da cewa yana da “ƙarfin gwiwar” samun nasara a zaɓen.
Dokokin a Amurka sun ƙayyade zango biyu ne ga shugaban ƙasa, wanda hakan ke nufin Trump ba zai iya zarce shekarar 2028 ba idan ya samu nasara.
A baya ba a cika jin Trump yana batun yiwuwar faɗuwa zaɓe ba, amma a cikin kwana huɗu da suka gabata, wannan ne karo na biyu da yake bayyana irin wannan maganar.
A wani taro da cibiyar Isra’ila da Amurka ta shirya a ranar Alhamis, ya yi maganar yiwuwar faɗuwar zaɓe, inda ya ce idan ya faɗi, hakan ba zai rasa nasaba da rashin goyon bayan Yahudawa ba.
Ya ce, “Sun san abin da zai faru idan ban ci zaɓen nan ba kuwa?” in ji shi kamar yadda kafofin watsa labarai da dama suka ruwaito.
“Ya kamata Yahudawa su yi wani abu saboda idan yanzu aka ce ina da goyon baya kashi 40 ne, hakan na nufin kashi 60 na wajen maƙiya ne.”
Sai dai kwamitin yaƙin zaɓen Kamala sun yi watsi da jawabin na Trump.


