Mason Greenwood ya amince wa abokansa cewa ba zai sake buga wa Manchester United wasa ba, in ji jaridar UK Sun.
An yi watsi da tuhumar fyade da cin zarafi da ake yi wa Greenwood a watan Fabrairu.
Amma tun daga lokacin United ta fara binciken cikin gida, inda ta hana dan wasan komawa filin wasa.
Ana sa ran dan wasan mai shekaru 21 zai shiga cikin tawagar Erik ten Hag bayan an yi watsi da tuhumar kuma ya yi takaicin rashin ci gaba.
A yanzu dai, ba a bar Greenwood ya koma atisaye tare da Red Devils ba, duk da cewa yana samun fam 70,000 a kowane mako.
Kwantiraginsa na yanzu a Old Trafford zai kare ne a lokacin bazara na 2025.