Shugaban majalisar dattawa ta 9, Dr Ahmad Ibrahim Lawan, ya jaddada kudirin sa ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda ya karyata rahotanni da fastoci da ake yadawa na cewa ya shirya ficewa daga jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar Social Democratic Party, SDP.
Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattijai kuma a halin yanzu shine shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, ya bayyana a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ezrel Tabiowo ya sanyawa hannu kuma ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata cewa “rahotannin gaba daya karya ne, marasa tushe, kuma ba su da wani inganci.”
Sanarwar ta ce Lawan “ya ci gaba da kasancewa mai tsayin daka kuma mai aminci a jam’iyyar APC, jam’iyyar da ya ke alfahari da ita da kuma bayar da gudunmawarsa tun bayan kafuwarta”, ta kuma kara da cewa “har yanzu ya kasance babban mai ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, kuma zai ci gaba da hada kai da jam’iyyar da gwamnati wajen ganin an cimma nasarar manufofinsu na gama-gari.
“Idan za’a iya tunawa, a tsawon shekaru ashirin da biyar yana siyasa a matsayin dan majalisar tarayya, Sanata Ahmad Lawan yana daya daga cikin ’yan siyasar Najeriya da ba su da tarihin sauya sheka tun daga farko.
“A shekarar 1999, an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai; sannan ya koma majalisar dattawa a shekarar 2007, a karkashin jam’iyyar All People’s Party (APP), wadda daga baya aka sauya mata suna ‘All Nigeria People’s Party (ANPP)’.
“Jam’iyyar ANPP na daga cikin ‘yan tsirarun jam’iyyu uku da suka hade zuwa jam’iyyar All Progressives Congress a ranar 6 ga Fabrairu, 2013.
“Sanata Lawan ya kasance mai cikakken imani da hangen nesa da ka’idojin jam’iyyar APC, kuma yana ci gaba da yin aiki tukuru tare da sauran shugabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar wajen karfafa jam’iyyar tare da ciyar da manufofinta na ci gaban al’ummarmu,” inji ta.
Sanarwar ta kuma kara jaddada cikakken goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa mai wakiltar jihar Yobe, Mai Mala Buni, “a kokarinsa na a yaba masa na samar da shugabanci na gari da inganta rayuwar al’ummar jihar”, yana mai cewa ya jajirce wajen yin aiki tare da shi domin cimma burin da aka sanya a gaba na jihar.
Har ila yau, Lawan ya nuna goyon bayansa sosai ga manufofi da sauye-sauyen gwamnatin shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana imaninsa kan kudirin gwamnatin na kawo sauyi a Najeriya da kuma magance kalubalen da kasar ke fuskanta.
“Muna kira ga jama’a da ‘yan jam’iyya da magoya bayansu da su yi watsi da wadannan jita-jita da fastoci marasa tushe, domin ba komai ba ne illa aikin miyagu da ke neman haifar da rudani da hargitsin da ba dole ba don tsara manufofin siyasa,” in ji sanarwar.