Dan wasan Gremio, Luis Suarez ya ce, ba zai koma wajen Lionel Messi a Inter Miami ba.
Tuni Messi ya tabbatar da cewa zai ci gaba da taka leda a gasar Major Soccer League (MLS) bayan ya bar Paris Saint-Germain a matsayin dan wasa kyauta.
Tun a wancan lokaci ake ta rade-radin cewa Suarez zai koma Barcelona, wanda suka yi wasa tare a Barcelona tsawon kaka shida.
Sai dai dan wasan mai shekaru 36 ya dage cewa zai mutunta kwantiraginsa da Gremio.
“Wannan karya ne, ba zai yiwu ba,” in ji Suarez ga jaridar Uruguay El Observador game da rahotannin.
“Ina matukar farin ciki a Gremio kuma ina da kwantiragi har zuwa 2024.”
Suarez ya zura kwallaye 11 sannan ya taimaka aka zura kwallaye takwas a wasanni 24 da ya buga wa Gremio.