Xabi Alonso ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zama kocin Bayer Leverkusen a kakar wasa mai zuwa.
Tsohon dan wasan tsakiya na Spain yana jan hankalin Bayern Munich da Liverpool kafin bazara.
Amma da yake magana da manema labarai a ranar Juma’a, Alonso ya bayyana cewa yana farin cikin ci gaba da kasancewa tare da shugabannin Bundesliga.
Ya ce: “Ina da manyan ma’aikata da ke taimaka mini kowace rana don yin aiki mafi kyau, ingantawa da kuma shirya kungiyar – kuma tabbas, ‘yan wasan suna ba ni dalilai masu yawa don ci gaba da yin imani da kungiyar.
“Jajircewarsu, sha’awarsu da yunwa, na ganin aikina bai kare a nan ba.
“Idan aka hada duk waɗannan abubuwan, wannan muhimmin shawarar da na yi imani ita ce ta dace. Har yanzu ni matashi ne kuma lokaci zai nuna, amma yanzu ina farin ciki.”