Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata, Atiku Abubakar, ya ce duk da shan kaye da ya yi a zaben, zai ci gaba da taka rawa a siyasar Najeriya.
Ya yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki musamman masu tasowa domin ganin kasar ta kai ga cimma burinta.
Atiku ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Sabanin rade-radin da ake yi cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya kawo karshen siyasarsa bayan yunkurin zama shugaban kasa da dama, Atiku ya bayyana cewa ba zai tafi ba.
Ya ce, “Idan kuna tunanin zan tafi, ku manta da shi. Matukar ina numfashi, zan ci gaba da yi wa ’yan Najeriya aiki don isa ga karfinsu.
Ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da yin magudi a zaben da ya gabata, yana mai jaddada cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba.
Atiku ya kuma ce INEC ta dauki bangare yayin da take kare sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da kotun koli.