Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya ce, ba zai gudu daga Najeriya ba, saboda tsoron hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, bayan ranar 29 ga watan Mayu da wa’adinsa ya kare.
Wike ya ce, zai yi farin ciki da karrama EFCC idan aka gayyace shi a karshen wa’adinsa a ranar 29 ga watan Mayu.
Gwamnan ya mayar da martani ne kan fallasa kwanan nan da Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya yi na cewa, hukumar za ta kama wasu gurbatattun gwamnonin da wa’adinsu ya kare a ranar 29 ga watan Mayu.
Karanta Wannan: Ina goyon bayan dakatar da Ayu daga PDP – Wike
Sai dai Wike ya ce, bai damu da barazanar kama gwamnonin ba a karshen wa’adinsu a ranar 29 ga Mayu.
Gwamnan yayi magana a shirin karin kumallo na Channels Television, SUNRISE a ranar Litinin.
Wike ya sha alwashin ba zai gudu daga Najeriya kwanaki kafin rantsar da wanda zai gaje shi kamar yadda wasu tsofaffin gwamnoni suka yi a baya.
“Ba zan gudu ba saboda EFCC. Me yasa zasu gayyace ni? Idan sun gayyace ni, zan girmama gayyatarsu. Ba zan gudu ba,” in ji Wike.