Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya ce, ba shi da wani abu na kashin kansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa yana sukar shugaban kasa ne kawai kan rashin iya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar da kuma Najeriya.
Gwamnan ya mayar da martani ne ga wata sanarwa da Shugaban Ilimin Manyan Makarantu na Majalisar Wakilai, Aminu Suleiman Goro ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a lokacin kaddamar da wasu ayyuka a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Makurdi.
An ruwaito cewa shugaba Buhari ya roki gwamna Ortom da ya yi kokarin amincewa da manyan ayyukan gwamnatinsa a jihar Benuwe maimakon yi masa zagon kasa.
Amma Gwamnan a jawabinsa a ranar Asabar, 1 ga Oktoba, 2022 a hidimar bikin Independence Day a Interdenominational Church wanda gwamnatin jihar ta shirya tare da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ya jaddada cewa, ba shi da wani abu na kashin kansa a kan shugaban kasa face ya damu da kashe-kashen da ake yi wa al’ummarsa.
Taron ya gudana ne a cocin Faith Cathedral of All Nations Evangelism Ministry, Old GRA, Makurdi.
Gwamnan ya tambayi dalilin da ya sa ya daina sukar Shugaban kasa a kullum ana kashe al’ummar Binuwai, ba tare da gwamnatin tarayya ta iya kawo karshen hakan ba, yana mai jaddada cewa, “Ba zan daina suka ba har sai an daina kashe-kashen,” Gwamnan ya bayyana.