fidelitybank

Ba zan ce komai ba a kan dambaruwar ricikin siyasar gwamnatin Kano – Kwankwaso

Date:

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP a 2023, kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ya yanke shawarar yin shiru kan rikicin cikin gida da ke ci gaba da yi wa jam’iyyar barazana a jihar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa da ke Miller Road a Kano, inda ya ce babu abin da zai ce game da lamarin.

“Bana son magana, don Allah. Kar ka ja ni cikin abin da bai kamata a ja ni ba. Shugaban jam’iyyar ya yi magana kuma yana magana, ku kai gare shi,” inji shi.

Ku tuna cewa an samu rikicin cikin gida tsakanin jam’iyyu wanda ya kai ga dakatar da sakataren gwamnatin jihar, SSG, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol.

Shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce dakatarwar ta biyo bayan zargin rashin mutunta jam’iyyar, cin zarafi da mukami da kuma rashin biyayya ga jam’iyyar.

Dakatarwar ta zo ne sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sulhu tsakanin SSG da ‘yan mazabarsa.

Haka kuma SSG din ya nesanta kansa daga yakin neman raba kan Gwamna Yusuf da Kwankwaso a karkashin sunan ‘Abba Tsaya da Kafarka’ ma’ana; Abba ya tsaya da kafarka.

breaking news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp