Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alwashin cewa ba zai bari wani mahaluki ya kawo katsalanda ba a zabukan 2023 da ke tafe a Najeriya.
Buhari ya ce, shugabancin da ba a ginata kan turbar gaskiya ba ba za ta kawo kasar alfanu ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tarbar gwamnonin jamâiyyar APC da gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ke jagoranta a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban ya kuma ce a karkashin shugabancinsa, zai ci gaba da mutunta âyan Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa kuriâunsu sun yi tasiri, saboda suna da yancin zabar shugabannin da suke so a dukkan matakai.


