Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da tabbacin cewa, ba zai bari iyalansa su yi masa katsalandan a harkokin tafiyar da jihar ba.
Ya yi wannan alkawari ne bayan karbar takardar shedar dawowar sa a Kano, inda ya yi nuni da cewa babu yadda za a yi iyalansa su taka rawar gani a harkokin gwamnati domin hakan zai zama tamkar na iyali.
Karanta Wannan: INEC ta miƙawa Abba Kabir shaidar katin cin zaɓen gwamnan Kano
“Babu yadda za a yi in bar iyalina su shiga cikin gwamnati ta, saboda rantsuwar da na yi, na yi shi kadai ba tare da su ba, ma’ana ba sa cikin gwamnati”, inji Abba.
Zababben Gwamnan, wanda ya fito daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya yi wa mazauna Kano alkawarin cewa, zai maida hankali ga jihar gaba daya, tare da mika lokacinsa domin daukaka darajar rayuwar al’umma.
Ya ce zai bunkasa harkar noman ruwa, kuma ilimi zai samu kulawa, yana mai tabbatar da cewa, za a yi garambawul ga harkokin mulki a jihar Kano.