Sabon sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya sha alwashin yin aiki da shugaba Bola Tinubu.
Akume ya kuma yi alkawarin ba zai bata wa ‘yan Najeriya da Tinubu kunya ba wajen gudanar da ayyukan sa.
Ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan an rantsar da shi a matsayin sabon SGF a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar Akume: “Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zan yi iya kokarina, ba zan ba shugaban kasa kunya ba, ba zan ba kasar nan kunya ba, kuma ba zan bata jam’iyya ta ba.
“Na yi imanin ’yan Najeriya za su samu cikar nauyin da ke wuya na yayin da na sauke hakan don amfanin kansu. Abin alfahari ne in yi wa kasa hidima, kuma na gamsu da cewa Allah Madaukakin Sarki ya jagorance ni, zan yi iya kokarina, kuma ’yan Najeriya za su samu ribar dimokuradiyya.
“Ni mutum ne wanda ya dade a wurin kuma na san mutumin da muke yi wa hidima, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa kuma dole ne mu bi sawun sa.
“Bai taba shiga dakin kallo ba, wanda ko da yaushe cike yake da masu suka. Ya kasance yana cikin fage, inda masu yi suke. Shi mai aikatawa ne, don haka dole ne mu yi tambari. Bai kamata mu taba yin kasa a gwiwa ba.”