Ministan harkokin wajen Rasha Segei Lavrov, ya ce kasarsa ba za ta yi amfani da makaman nukiliya a Ukraine ba.
Yayin da yake magana a tashar talabijin ta Indiya Today ta kasar Indiya, Mista Lavrov ya ce “makaman da aka saba amfani da su ne kawai za mu rika kai hari da su”.
Mista Lavrov ya kuma ce yakin ya shiga wani mataki bayan da dakarun Rasha suka mayar da hankalinsu ga yankin gabashin kasar:
“Mun fara wani sabon babi na ayyukan tsaro, kuma na tabbatar zai kasance mai muhimmanci sosai ga biyan muradunmu.”