Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa yarda da maganar tsagaita wuta a yaƙi tsakaninta da Hamas ba.
“Kamar yadda Amurka ba ta yarda da tsagaita wuta ba bayan harin bam kan Pearl Harbour ko kuma harin 9 ga watan Nuwamba, Isra’ila ma ba za ta yarda da tsagaita wuta kan Hamas ba bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba,” in ji shi yayin jawabin da ya kammala ɗazun nan.
“Kiraye-kirayen tsagaita wuta na nufin Isra’ila ta miƙa wuya ga Hamas, ta miƙa wuya ga ta’addanci,” a cewarsa.
“Littafin Injila ya ce akwai lokacin zaman lafiya, da kuma lokacin yaƙi. Wannan lokacin yaƙi ne.
“Yaƙi ne game da makomarmu. A yau muna yaƙi ne tsakanin dakarun al’umma da kuma dakarun rashin imani.”