Hukumomin ƙasar nan ta ce, ba za ta yarda da duk wata shaidar karatu ba kan likitanci da ɗalibai suka samu daga jami’o’in Ukraine a shekarar 2022, a cewar Majalisar Likiitoci ta ƙasa ta Nigerian Medical and Dental Council (MDCN).
Majalisar wadda ke sa ido kan harkokin lafiya a Najeriya ta ce, an ɗauki matakin ne saboda yaƙin da ake yi a ƙasar, sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa, abin da ya sa aka rufe azuzuwa na jami’o’i da manyan makarantun ƙasar.
“Muna sanar da jama’a cewa MDCN ba za ta yarda da shaidar karatun digiri ba kan harkokin lafiya da aka samo daga Ukraine a 2022 har sai harkokin karatu sun koma yadda aka saba,” in ji wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na Twitter.
Da yawa daga cikin jami’o’in na ci gaba da karatu ta intanet, matakin da MDCN ta ce, ya saɓa wa manhajar koyar da likitanci. In ji sanarwar.