Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta yi gargadin cewa, ba za a lamunta da ci gaba da kashe-kashen da ake yi wa ’yan Arewa a yankuna da dama na Kudancin kasar nan ba.
Daraktan Yada Labarai na Kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya yi kira ga gwamnatoci da al’umma da jami’an tsaro da su kare ‘yan Arewa mazauna Kudu.
Zauren ya ja hankali kan illolin da ke tattare da ta’azzara da tada hankali.
Ta nuna matukar damuwarta kan abin da ta bayyana a matsayin yadda al’amura ke kara ta’azzara, na cin zarafi da kashe-kashen ‘yan Arewa a yankuna da dama na Kudu.


