Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta ƙasa, IPMAN, ta ce mambobinta ba za su iya sake siyar da mai akan Naira180 kan kowace lita.
IPMAN ta ce, sun yanke shawarar ne saboda yanayin kasuwanci, wanda ya sanya aka rufe wasu tashoshin.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Legas, shugaban, Akin Akinrinade, ya ce, farashin da aka kayyade bai dace da mambobinsu ba.
“Mambobinmu ba za su iya siyar da su a kan Naira 165 ba. Hasali ma, babu wani dan kasuwa mai hankali a wannan sana’ar da zai iya siyar da kasa da Naira 180 kowace lita,” inji Akinrinade.
A makon da ya gabata ne shiyyar IPMAN ta kudu maso yammaci, ta yi barazanar cewa, mambobinta za su rika sayar da man fetur a kan Naira 180 kan kowace lita.
Dogayen layukan man fetur sun sake kunno kai a Legas a ranar Litinin, bayan karanci da aka samu a Ibadan, jihar Oyo da sauran sassan kasar.
Karancin ya kara rura wutar jita-jitar da ake yadawa cewa, ‘yan kasuwa sun shiga yajin aiki don sanya sabon farashin sayar da man fetur.