Hukumar jin daɗin ‘yan sanda ta ƙasa, ta bayyana cewa, ta jingine tuhumar da ta shafi mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, saboda wasu dalilai.
Hukumar ta faɗi haka ne ta bakin shugaban ta, Musiliu Smith, a wurin taronta karo na 14 wanda ya gudana a Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa,. Mista Smith ya yi bayanin cewa, hukumar ba za ta ɗauki wani mataki kan Kyari ba a halin yanzun, har sai an kammala binciken da ta bayar da umarnin a sake yi.