Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, ya yi dogon tattaunawa da iyalan ‘yan Isra’ila biyu da ake garkuwa da su a Gaza, bayan sakin wani bidiyo da ke nuna mutanen su biyu cikin yanayi na galabaita.
Mista Netanyahu ya ce ya nuna wa iyalan, Evyatar David da Rom Braslavski yanayi na kaɗuwa da ya shiga – da alkawarta cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba, har sai an sake dukkanin sauran mutanen da ke hannun Hamas.
Sannan ya bukaci dukkanin ‘yan ƙasar su yi Allah-wadai da Hamas.
A jiya Asabar dubban mutane sun fito zanga-zangar mako mako da aka saba yi a TelAviv domin neman ceto sauran mutanen da ake riƙe da su a Gaza.