fidelitybank

Ba za mu yi gaggawar amincewa da ‘yan takara ba – Kungiyar Dattawan Arewa

Date:

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana dalilin da ya sa ba ta amince da duk wani dan takarar shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar ta NEF, ya ce kungiyar ba za ta yi gaggawar amincewa da duk wani dan takarar shugaban kasa ba, duk da cewa zabe na karatowa.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a lokacin da ya fito a matsayin bako a wani shiri kai tsaye da gidan Talabijin mai zaman kansa na Afrika (AIT).

Baba-Ahmed ya ce, NEF na tantance manyan ‘yan takara ta fuskar abin da suke yi da kuma fadin su.

Ya ce kungiyar ta arewa tana kuma tantance ‘yan takarar wasu kujeru da suka hada da ‘yan majalisar tarayya da na gwamnoni. “Mun yi imanin cewa mulki ba wai mutum daya ne kawai ba, shi ya sa ba mu yi gaggawar cewa wannan shi ne dan takararmu ba saboda mutum daya ba zai iya canza kasar nan ba,” inji shi.

Ya ce ‘yan Najeriya na bukatar “shugaban kasa mai jajircewa” da zai dauki matakin da ba zai yi farin jini a tsakanin jama’a ba. A cewar Baba-Ahmed, kasa mafi yawan al’umma a Afirka ba ta bukatar shugaban kabila ko kuma wanda aka zabe shi bisa addini.

sun newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp