fidelitybank

Ba za mu taɓa yin sulhu da ƴan ta’adda ba – Gwamnan Zamfara

Date:

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada alkawarin gwamnatinsa na cewa ba za ta taba yin sulhu da barayi da ‘yan fashi da makami ba domin samar da zaman lafiya.

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa Malam Mani Mumuni ya ce gwamnatinsa a shirye take ta maraba da duk wata jam’iyyar adawa a fafutukar kawo karshen rashin tsaro a jihar, inda ya ce shi ba jam’iyyar PDP kadai ba ne, illa jihar baki daya.

“Ba ni kadai ne Gwamnan PDP ba, ni ne Gwamnan Zamfara gaba daya, don haka kowa ya cire wariya daga gwamnatina,” ya kara da cewa.

Ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke kan zabensa nasara ce ga dimokradiyya da kuma ci gaban kasa baki daya.

“Ba komai ko wanene APC ko PDP, nine gwamnan jihar Zamfara ba tare da la’akari da jam’iyya ko kabila ba”

Dauda Lawal ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishinsa da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce bangaren shari’a ya tabbatar da amincinsa a matsayin fata na karshe ga talaka, ya kuma yaba musu da hangen nesa.

Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin mai ci a shirye take ta kawo karshen rashin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa ba za a amince da duk wani aiki na cin amana ba.

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp