fidelitybank

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Date:

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi ne ta daƙile barazana biyu daga gwamnatin Iran – barazanar makaman nukiliya da ta manyan makamai masu linzami, kuma ya ce Isra’ila ta cimma burinta.

Ya ce Isra’ila ba za ta taba barin Iran ta samu ƙarfin ƙera makamai masu linzami 20,000 ba, ”saboda haka muka dauki matakin lalata fasaha da ƙarfinsu, kuma wannan shi ne abin da rundunar sojin Isra’ila ke yi a yanzu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: ”Mun bude hanyar shiga Tehran. Nan gaba kadan za ku ga jiragen yaƙin Isra’ila, da sojojin sama na Isra’ila, da matuka jiragenmu, a sararin samaniyar Tehran.”

Netanyahu ya ce Isra’ila za ta kai wa Iran hari a duk inda ta nufa, bayan da Iran din ta mayar da martani kan harin da Isra’ilar ta kai mata ranar Juma’a.

Iran ta harba makamai masu linzami cikin sassan biranen Isra’ila a jiya dadaddare, inda hukumomin Isra’ilar suka ce harin ya kashe mutum uku.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...
X whatsapp