Jam’iyyar PDP a jihar Ribas ta bayyana cewa, duk wani yunkuri na ci gaba da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar zai haifar da tashin hankali.
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a Fatakwal a ranar Juma’a, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Aaron Chukwuemeka, ya sake jaddada cewa PDP ba za ta shiga zaben ba.
Chukwuemeka ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bisa hana rajistar masu kada kuri’a daga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas, RSIEC, yana mai bayyana ci gaban a matsayin babban koma baya ga harkokin zaben.
Ya kuma yabawa ‘yan sandan Najeriya bisa kin shiga zaben.
Shugaban jam’iyyar PDP ya bukaci gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, dan jam’iyyar PDP, da ya dakatar da shirye-shiryen gudanar da zaben.