fidelitybank

Ba za mu saurara wa Rasha ba har idan Trump suka yi sulhu da Putin – Ukraine

Date:

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ba za ta amince da duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka da Rasha suka cimma kan yaƙin Ukraine ba, matsawar ba a sanya ta cikin zaman ba.

 

A jiya ne Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce a lokacin zantawarsa da Putin ta waya sun amince da tattaunawa domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin.

 

Yayin da yake martani kan wannan batu, Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce ”yana da kyau kowa ya fahimci cewa ba za mu yarda ayi komai yassa Rasha ta tsara ba,…”kamar yadda kamfanin dillancin labari na Reuters ya ruwaito.

 

Zelensky ya ƙara da cewa bai tattauana batun Nato da Trump ba, amma ya sani cewa Amurka ba ta muradin Ukraien ta zama mamba a ƙungiyar.

 

A wani labarin mai alaƙa wasu ƙasashen Turai bakwai sun fitar da sanarwa buƙatar taka rawa a duk wata tattaunawa da za a yi a kan makomar Ukraine nan gaba.

 

Trump ya ce zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Saudi Arabia, inda za su tattauna a kan yaƙin, to amma kuma Fadar White House, ta nuna alamun cewa babu wani shiri na wata ƙasar Turai ta kasance a wajen taron, ciki har da Ukraine ɗin kanta.

 

Sai dai duk da wannan sakataren tsaro na Amurkar ya musanta cewa hakan alama ce ta cin amanar gwamnatin Ukraine.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp